Rike Karatu ,gaskiya da Amana shine martaban Arewa: Omer Aliyu Tilde

Wani hazikin matashi a dake garin Tilden Fulani,a karamar hukumar Toro na Jihar Bauchi Omer Aliyu Tilde Wanda yayi fice wajen sokaci akan abubuwan da suka shafi yau da kullum musamman makoman Arewa a yanar gizo . Matasa Arewa wata kafa ce dake kokarin wayar matasan yankin arewancin Najeriya kai domin samun daidaito da cigaban yankin ta fannin ilimi mai anfani da habbaka tattalin arziki a hiran su ta musumman da wanan matashi sun tautauna batutuwa da dama.

Ga dai yadda hiran tasu ta kasance daga bakin Wakilin Tildetimes dake zaune a garin Bauchi wato Abdulrahman Kirfi.

A wannan Rana ne cikin wannan lokaci muke farin cikin kasancewa tareda Babban Baqo mu na wannan Satin.

Matasa AREWA: Rankashidade Barka da warhaka, Dafatan kana lafiya, kuma gida lafiya?

Barka da safiya. Da yardar Allah, ina cikin koshin lafiya.

Farko dai zamuso kabada takaitaccen tarihi ka, domin masu bibiyar wannan zaure zasu So ji?

Suna na Omer Aliyu Tilde. Ina da kimanin shekara 25. Na tashi a garin Tilden Fulani. A nan nayi primary har zuwa JSS. Daga nan na tafi FGC Kiyawa. A karshe na gama karatun secondary a Dolphin Maria College, Bauchi.

Na samu kwalin Degree dina a Ghana, daga Jami’ar Kwame Nkrumah University of Science and Technology.

Matasa AREWA: Daman can Karatun tattalin arziki (Economics) Shine gurin ka, koko wani dalilin yasa ka karance shi?

Da farko na fara karanta Architecture a Federal Polytechnic Bauchi. Amma da na samu daman barin Bauchi, sai na koma fanin tattalin arziki ganin karancin yar Arewa a wannan fanin. Na ga cewa ya kamata ace an samu kwararru yan Arewa a wannan fanin.

Matasa AREWA: A Matsayin ka na Dalibi, kuma Matashi shin ka taba riqe wani mukami tun daga ajin furame, har I zuwa yanzu, kuma wane irin rawa kataka wurin kawo canji?

A’a ban taba rike mukami ba har zuwa yau.

Matasa AREWA: Ko zamu iya jin Banbanci tsakanin Karatu a Ghana da Najeriya, Meyasa ake zuwa Ghana dukda Jami'o'i da muke dasu a Najeriya?

A gani na babu wani banbanci sosai illa rashin cunkoso wajen koyarwa.

Matasa AREWA: Rankashidade Kanada Aure?

A’a bani da aure.

Matasa AREWA: Ko ka taba Zuwa Hajji ko Umrah?

A’a, har yau Allah bai nufe ni da zuwa ba.

Matasa AREWA: Wane irin kalan Abinci yafi burgeka (Favorite food)?

Dan wake

Matasa AREWA: Rankashidade Menene Saqo ka ga 'yan uwa Matasa AREWA? Kamar meya kamata muyi domin dawo da martabar mu a idon kasa Najeriya?

Sako na guda biyu ne.

Na farko shine mu rike karatu hannu biyu. Karatu shine muhimmin abun da aka san iyayen mu dashi. Walau karatun boko ko na addini. Duk suna da amfani.

Na biyu kuma shine rikon gaskiya da amana. Gaskiya na tafiya da martaba. Duk inda kuwa aka rasa gaskiya to dole a rasa martaba.

Nagode da lokacin ku.

Comments

Popular posts from this blog

Plateau North Re-rerun: Parties await Tribunal Judgement

Frontline YAN National Speaker Aspirant Amb. Sadiq Tour southern Nigeria, seek support

Dr. Abubakar Muhammad Bello to Receive NANS 'Grand Leader of Masses' Award