ABINDA YA KAMATA MUNANE SU SANI GAME DA COVID-19: FURERA BAGEL

Ina so ne in jawo hankalin jama'a a kan wannan annoba da ake fama da ita Mai suna Corona. Musamman wasu da har yanzu suke ganin cewa bata zo kasar mu ba kuma baza ta taba zuwa ba. Duk da a kullum ana fadin yawan jama'a da suka kamu da cutar a fadin duniya da kuma nan gida Nigeria.

Kaman yanda masana da yawa suka fadi, an yi annoba da yawa a duniya tun shekaru aru aru da suka wuce. Sabo da haka ba wani sabon abu bane.

Misali, an yi annobar da ake kira Justinian(541-542), wadda turawa suke ganin ma daga Afirka ta fito Sannan ta ketara kasashen Turai. Ita wannan annobar da ta isa birnin Santambul a shekaranjiya 541 A.D, a kullu yaumin Sai ta kashe mutum dubu goma. A fadin duniya ta kashe mutum Miliyan 25.

Akwai annobar black death (1346-1353), Wato bakar mutuwa wacce ta kashe mutane Miliyan 75 zuwa 2000. Da kuma annobar Cholera (1852-1860), Wadda ta fito daga kasar Indiya ta kuma yadu sosai a duniya inda ta yi silar mutuwar mutane Miliyan daya a fadin duniya.

Sai kuma Spanish flu (1918-1920), wadda a sati 25 na farkon yaduwarta kawai ta kashe mutane Miliyan 25. Ana ganin a karshenta mutane Miliyan 50 ne suka rasa rayukansu.

Wannan annobar ta Spanish flu har Kasar Nigeria ta zo,  ta kuma yadu a wasu garuruwa na arewa, inda a Kano an rasa rai 57,978 a lokacin yawan jama'ar Garin 2,749,727 ne.

A Bauchi an rasa rai 17,102. A Borno kuwa 10,000 mutane aka rasa. Sokoto mutum dubu talatin, Yola mutum dubu sha daya,  Zaria 6,776 Ilorin 28,884 da dai sauransu, Kamar Yada aka nuna a jaddawali na kasa.

Ba Wai fatan mutuwa nake yi ba da na kawo wannan, a'a Ina so in nuna wa jama'a ne musamman wadanda basu yarda da cewa annobar zata iya zuwa nan ba, da su san cewa an taba yi kuma ga illar da ta yi mana lokacin ma da bamu da yawa sosai.

Sabo da haka don Allah a kiyaye. A bi dokokin da masana lafiya suka gindaya mana don abin ya zo mana da sauki.

Allah ya bamu ikon yi ya kuma kare mu baki daya.

Comments

Popular posts from this blog

Dankwambo/Amtai political feud, Group calls for quick Security interventions.

Comr. Auwal Suspended from office as National President,Yobe State Students.

Plateau North Re-rerun: Parties await Tribunal Judgement